✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda EFCC za ta titsiye Betta Edu

Betta Edu za ta amsa tamboyoyi ne washegarin da Sadiya ta kwana  tana amsa tambayoyi kan wata badakalar ta daban a hannun EFCC

A yau talata Hukumar Yaki da Masu Karya tattalin Arzikin Kasa (EFCC) za ta titsiye Betta Edu, Ministar Jinkai da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar kan badakar kudade.

Betta Edu za ta amsa tamboyoyi ne washegarin da aka dakatar da ita, aka kuma hana ta yin ido hudu da Shugaba Tinubu, aka soke izininta na shiga Fadar Shugaban Kasa.

Tuni shugaban kasa ya umarci Ministan Kudi, Wale Edun ya jagoranci kwamitin bincikar Betta Edu da kuma toshe duk wata kafar da ake almundahana a harkar kudin tallafin gwamnati a ma’aikatar.

Kasa da minti 30 da dakatar da Betta Edu ne EFCC ta sanar da gayyataeta kan badakalar karkatar da kudaden tallafin masara karfi na jihohi hudu.

A ranar da aka dakatar da ita, magabaciyarta, Sadiya Umar-Farouq, ta kai kanta ofishin hukumar EFCC, inda ta kwana  tana amsa tambayoyi kan wata badakalar ta daban ta Naira biliyan 37, zargin da ta musanta.

A ’yan makonnin nan dai zargin almundahana ya dabaibaye ma’aikatar jinkai, inda ake bincike kan harkokinta na shekaru shida da suka gabata.

A baya-banan nan aka bankado bakaladar karkatar da kudaden tallafin masu karamin karfi kimanin Naira biliyan 44 daga Ofishin Kula da Rabon Tallafin Dogaro da Kai.

Ana zargin shugabar hukumar, Halima Shehu, ta tura kudaden zuwa asusun ajiyar wasu mutane da kamfanoni ba bisa ka’ida ba.

Amma Halima ta ce ta yi haka ne bisa tursasawa da matsin lamba daga Betta Edu; duk da haka shugaban kasa ya dakatar da ita, tare da ba da umarnin a bincika lamarin.

Daga bisani kuma wata sabuwa ta kunno kai bayan Betta Edu ta aike wa Ofishin Akanta-Janar na Kasa takardar neman ofishin ya tura Naira miliyan 585 zuwa asusun wata mata.

Betta ta ce matar akanta ce a ofishin kula da tallafi a wasu jihohin kudu hudu, amma duk da aka ofishin Akanta-Janar ya ki, da cewa yin hakan ba aikinsa ba ne.

Akwai kuma zargin facaka da kudaden ma’aikatar bayan bullar wata dakarda dauke da sa hannun Betta Edu na biyan kudin tafiyar aikin jami’an ma’aikatar zuwa wani fili jirgin sama da babu shi a Jihar Kogi.

Zarge-zargen dai suka sa aka yi ca a kan lamarin gami da kira ga shugaban kasa ya dakatar da ita, ya sa a binciki lamarin.