Ranar Barci ta Duniya ranar ce da kwamitin ranar barci ya kirkira don wayar da kai da kuma warware matsalolin da ke da alaka da barci.
Ana gudanar da Ranar Barci ta Duniya ce a duk ranar 18 ga watan Maris na kowace shekara.
- Kotu ta yi watsi da bukatar dakatar da babban taron APC
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Mutane Ke Kashe Kansu Saboda Soyayya
An fara gudanar da bikin ranar ce a watan Maris din 2008, kuma yanzu haka sama da kasashe 70 ne ke gudanar da bikin a duk shekara.
Likitoci irin su Liborio Parrino da Antonio Culebras, su ne mambobi na farko kungiyar barci ta duniya, kuma mutane na farko da suka asassa ranar barci ta duniya.
Wasu na iya ganin barci ba a bakin komai ba, saboda yana daga cikin jerin abubuwan da jama’a ke yi koyaushe, amma yana da matukar muhimmanci wanda rashin samun shi yadda ya kamata na iya haifar da tawaya ga lafiyar jikin jikin dan Adam.
An ware ranar ce don fadakar da jama’a game da muhimmancin da ke tattare da barci a fadin duniya, tare da nuna musu alfanun da yake haifarwa ga rayuwar mutane ta yau da kullum.
A cewar kungiyar barci ta Amurka, akalla mutum miliyan 50 zuwa 70 ne ke fama da matsaloli da ke da alaka da barci a fadin duniya.
Sannan kungiyar ta ce sama da mutum miliyan 25 ne ke fama da rashin isasshen barci a duniya.