A ranar 19 ga watan Maris ta kowace shekara ce aka ware a matsayin Ranar Barci ta Duniya domin wayar da kai game da muhimmancin yin barci ga lafiya.
An ayyana ranar ce domin fahimtar da jama’a illar wasu aikace-aikace da ke tauye hakkin samun barci, da kuma matsalar da hakan ke yi wa lafiya.
- Abin da ya sa Dala ta sake tashi zuwa N485
- Abin da ya sa ’yan mata ke son auren mazan da suka manyanta
Tun bayan ayyana ranar a shekarar 2008 masana lafiya a bangaren lafiyar barci ke jan ragamar wayar da kai cewa shaci-fadi ne ake ake bazawa cewa babu ruwan rashin barci da lafiyar ciki.
Aminiya ta tattaro muku wasu muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da muhimmancin barci ga lafiyarku:
- Samun lafiyayyen barci na da matukar muhimmanci ga lafiya.
- Lafiyar barci alama ce ta ingancin rayuwar mutum da ma al’ummarsa.
- Yana da kyau ka samu isasshen barcin da zai sa ka samu hutawa da karin annashuwa.
- Barci mai nauyi abu ne da ake bukatar mutum ya rika samu.
- Yin isasshen barci na taimakawa wajen gudanar da shu’uri.
- Karancin barci daya ne daga cikin matsaloli masu barazana ga lafiya da ingancin rayuwar kashi 45% na al’ummar duniya.
- Masu samun barci yadda ya kamata sun fi samun fara’a da nishadi da karsashi.
- Yin barci a-kai-a-kai na taimaka wa karin basira da hazaka.
- Rashin samun isasshen barci na kawo mantuwa, kasala da dusashewar tunani.
- Gajeren barci na iya kawo matsala ga lafiyar kwakwalwa.
- Isasshen barci na da muhimmanci a rayuwar mutum ta yau da kullum.
- Lafiyayyen barci na kara wa kananan yara lafiya.
- Yana kuma taimakawa wajen aikin jikin dan Adam na yau da kullum.