✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau Bakayoko zai sanya wa Chelsea hannu

Bayan kulob din Chelsea na Ingila da na Monaco da ke Faransa sun cimma matsaya a shekaranjiya Laraba, a yau Juma’a ne ake sa ran…

Bayan kulob din Chelsea na Ingila da na Monaco da ke Faransa sun cimma matsaya a shekaranjiya Laraba, a yau Juma’a ne ake sa ran Bakayoko zai rattaba hannu a kulob din Chelsea kamar yadda kafar watsa labaran wasanni a Faransa RMC ta ruwaito.

Idan hakan ta faru, kocin Chelsea Antoion Conte zai yi matukar farin ciki ganin yadda kulob din Manchester United suka yi masa shigar sauri wajen dauke dan kwallon Eberton Romelu Lukaku.

Bakayoko dai yana wasa ne a tsakiyar fili (Midfielder) kuma ana sa ran zai taimakawa kulob din wajen samun nasara a kakar wasa ta bana.