Karamar yarinyar nan mai baiwar lissafi a wani kauye a Jihar Kano, wadda ba ta zuwa makaranta, Saratu Dan-Azumi, ta samu tallafin karatu har zuwa kammala jami’a.
Tsohon Hadimin Shugaba Buhari kan Kafofin Sada Zumunta, Bashir Ahmda, ne ya dauki nauyin karatun Saratu bayan samun amincewar iyayenta.
- Yaron da ya yi irin Gadar Zulum ya ce burinsa shi ne zama injiniya
- Binciken kwakwaf: Su wane ne ’yan bindigar da suka addabi Zamfara?
Baiwar yarinyar mai suna Saratu Dan-Azumi ta dauki hankalin jama’a ne bayan fitar bidiyon inda ake mata tambayoyin lissafi, tana amsa su nan take, babu kuskure ba.
Mutane da dama sun yi ta tsokaci tare da bayyana jin dadinsu game da irin baiwar da Allah Ya yi wa Saratu, ’yar asalin kauyen Gwadayi, Gundumar Shagogo a Karamar Hukumar Gaya ta Jihar Kano.
Bayan kallon bidiyon ne Bashir Ahmad, yi ma ya fito daga Mazabar dan Majalisar Wakilai na Gaya/Ajingi/Albashu ya shiga neman Saratu da iyayenta.
Daga karshe dai, gidauniyarsa ta Bashir Ahmad ta gano iyayen yariyar, ta tattauna da su ta samu amincewarsu domin daukar nauyin karatun Saratu daga firamare har ta kammala karatun jami’a.
Bashir Ahmad, ya nemi tikitin takarar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu a Jam’iyyar APC, amma bai kai labari ba.