Saratu Garba, yarinyar nan mai shekara 11 mai baiwar lissafi a kauyen Gwadayi na karamar hukumar Gaya a jihar Kano, ta sami tallafin karatu daga Bankin Duniya.
Saratu ta samu tallafin ne a karkashin shirin tallafawa mata don su yi ilimi (AGILE), wanda Bankin ke daukar nauyi a jihar Kano.
- Shugaban Ukraine ya nemi tallafin Najeriya a yakinsu da Rasha
- Biranen Amurka 2 sun fara buga takardar kada kuri’a da Larabci
Malam Aliyu Musa, Jami’i Yada Labarai na shirin ne ya bayyana haka ga Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba.
Malam Yusuf wanda kuma shi ne Mataimakin Daraktan yada labarai na Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ya ce, ofishin kula da shirin na Bankin Duniya a jihar Kano ya bayar da umarni a zakulo yarinyar nan a kuma sa ta a makaranta.
“Sai a ka yi sa a, masu kula da shirin ilimin mata na AGILE na tsaka da ziyara zuwa masarautu biyar na jihar Kano don neman hadin kan sarakuna kan batun ilimin mata a jihar,” inji shi.
A yayin ziyararsu a masarautar Gaya ne jami’an suka yi wa Sarki bayanin yarinyar da kuma aniyarsu ta daukar nauyin karatunta, sai Sarkin na Gaya ya sa aka zo da yarinyar da kuma iyayenta har gabansu.
Nan take wakilin a Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano, Malam Haruna Mohammed Pandau, ya ba Saratu kayan makaranta da jakar makaranta da kuma wasu kayayyakin karatu.
Shi kuma Ado Tafida Zango, mai kula da shirin AGILE a jihar, ya ba ta Naira 20,000 daga aljihunsa don taimaka wa karatun nata.