✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaran jihar Edo sun fi sauran jihohi zuwa makaranta

An bayyana jihar Edo a matsayin jiha mafi karancin yaran da basu zuwa makaranta a Najeriya da adadin yara 79,446. A wata sanarwa da mai…

An bayyana jihar Edo a matsayin jiha mafi karancin yaran da basu zuwa makaranta a Najeriya da adadin yara 79,446.

A wata sanarwa da mai taimaka wa Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki a harkar watsa labarai Crusoe Osagie, ya fitar wannan ya biyo bayan rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana kwananan.

Rahoton hukumar NBS da ya sanar cewa jihar Edo nada adadin yara 79,446 da basu zuwa makaranta a Najeriya idan aka kwatanta da kuma jihar Bauchi mai adadi 1,239,759 wadanda basu zuwa makaranta, za a fahimci jihar Edo mafi karancin a sauran jihohin kasar.