Asusun Yara da Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce yara masu shekaru fiye da 11 su rika sanya takunkumi a wuraren da ake bukatar manya manya su sa domin kare su daga COVDI-19.
Shawarwarin da UNICEF da Hukumar Lafiyta ta Duniya (WHO) suka fitar ta jaddada bukatar masu shekaru shida zuwa 11 su sa kunkumi a wuraren da ke da yiwuwar samun cutar kamar makarantu da sauransu.
Sai dai sun ce akwai yiwuwar takunkumi “ya kawo cikas ga daukar ilimi ko ayyukan karatu”, ko da yake ba wajabta sanya wa ga yara suke neman yi ba.
Sanarwar ta ce babu bukatar sanya wa masu kasa da shekaru shida takunkumi domin ba lallai ne su iya sanyawa da cirewa daidai ba.
Idan kuma sun sa to a rika lura da su akai-akai, “A kuma rika sauraro da lura da fahimtarsu game da sanyawar”.
Makarin fuska bai kai kyalle amfani ba
Sun kuma ce makarin fuska da hanci mai kamar gilashi bai kai takunkumi na kyalle bayar da kariya daga cututtuka ba.
Hukumomin suka ce alkaluma sun nuna cewa yara da matasa masu kasa da shekara 18 su ne kashi daya zuwa bakwai cikin 100 na masu COVID-19 a duniya.
Har yanzu babu tabbaci kan a tsakanin manya da kananan yaran da suka kamu da cutar su wa suka fi daukar adadin kwayoyinta mafi yawa