✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yara 26.5m na fama da rashin ruwa a Najeriya —UNICEF

Yara 26.5m ne ke fama da matsalar rashin ruwa a Najeriya, inji UNICEF

Yayin da ake bikin Ranar Ruwa ta Duniya, Hukumar UNICEF ta ce kananan yara miliyan 26.5 a Najeriya ba sa samun tsaftacacen ruwa don amfaninsu.

Jami’in UNICEF a Najeriya, Peter Hawkins ne ya bayyana hakan, inda ya ce yawancin yaran na amfani ne da ruwan rafi, wanda ba ya gamsar da su yadda ya kamata.

Hawkins ya ce, a inda ake fama da karancin ruwa sakamakon kafewar rijiyoyi, yara ne suka fi shiga halin kaka-nika-yi, wanda hakan ke hana da dama daga cikinsu zuwa makaranta.

Ya kara da cewa rashin ruwan na hana yara dama samun damar tsaftace hannayensu, wanda a dalilin haka suke kamuwa da cututtuka barkatai.

Kididdigar UNICEF, ta nuna yadda karancin ruwa ke jefa rayuwar kananan yara cikin mawuyacin hali da kashi 80% a Gabashi da kuma Kudancin Afrika.

Har wa yau, Hawkins, ya bayyana cewa akwai jan aikin a gaban gwamnatin Najeriya na samar da ruwan da zai wadaci talakawan kasar.

Ranar 22 ga watan Maris ita ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bikin ranar ruwa ta duniya.