Wata matar aure mai shekara 37 ta haifi jarirai guda 10 a lokaci guda.
Matar mai suna Gosiame Thamara Sithole, ’yar garin Tembisa a lardin Ekurhuleni Gauteng na kasar Afirka ta Kudu ta kafa tarihin zama wadda ta haifi jarirai mafiya yawa a lokaci guda a duniya.
- An mari Shugaban Faransa a wurin nuna farin jininsa
- Yunwa ta sa daliban sakandare zanga-zanga a Gombe
Mijin mai jegon, Teboho Tsotetsi, ya ce, “Maza bakwai da mata uku ta haifa bayan juna biyun nata ya yi wata bakwai da mako guda.” Kafin wannan haihuwar, ta haifi tagwaye.
“Ina cike da farin ciki sosai da zumudi; Bari mu ci gaba da magana da safe, don Allah,” kamar yadda ya fada wa kafar labarai ta Pretoria News a kasar.
An ruwaito angon karnin yana cewa mai jegon ta haihu ne ta hanyar yi mata tiyata, bayan juna biyun nata ya yi mako 29.
A halin yanzu dai Gosiame Thamara Sithole ta karya tarihin Malian Halima Cissé, ’yar kasar Morocco wacce ta haifi jarirai tara a watan jiya.
A farkon shekarar nan ce likitoci sun fada mata cewa tana dauke da jarirai shida, amma da aka sake daukar hoton cikin sai ya nuna jarirai 10 ne.
A wata tattaunawa da aka yi da ita a lokacin, ta ce juna biyun ya wahalar da ita sosai, har takan share tsawon dare ba ta iya bacci sai yawan tunani.
“Na kadu sosai game da juna biyun nawa: Da farko akwai wahala sosai —Na yi laulayi, ga nauyin cikin; Abin sai dai godiya, amma na saba.
“Ba na jin zafi sosai yanzu, sai kadan-kadan; Ina rokon Allaha Ya sa na haifi dukkansu cikin koshin lafiya sannan ni da su duka mu rayu.
“Zan ji dadi idan hakan ya samu,’’ kamar yadda ta rika fada a baya.
“Yaya suke rayuwa a mahaifar? Za su rayu kuwa? Idan kuma suka fito a manne da juna ta ka ko ciki ko hannayensu, me zai faru?
“Sake-saken da na yi ta yi a zuciyata ke nan, har sai da likita ya tabbatar mini cewa mahaifata ta kara girma ta ciki.
“Allah Ya nuna ikonSa kan yadda jariraina suka zauna a cikin mahaifar ba tare da wata matsala ba,” a cewar Sithole.
Mijinta wanda ba shi da aikin yi, ya ce yanzu ya kawar da duk wata fargaba ya rungumi jariran hannu bibbiyu.
“Da farko ban yarda ba, amma yanzu ina jin kaina a matsayin guda cikin wadanda Allah Ya zaba, Ya albarkaci rayuwarsu, a yayin da mutane da dama ke neman samun ’ya’ya,’’ inji mijinta.
Sai dai jariran za su ci gaba da zama a cikin kwalbar asibiti zuwa wani lokaci kafin a sallame su.