✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yar shekara 12 ta lashe gasar Al-Kur’ani a Legas

Karamar yarinyar ta ciri tuta a rukunin masu tasowa, daga mutum 100 da suka nemi shiga gasar.

Wata yarinya mai shekara 12 mai suna Khadijat Sharafadeen ta lashe gasar karatun Al-kur’ani da aka gudanar a yankin Badagry na Jihar Legas.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa gasar musabakar wacce ake gudanarwa a kowanne watan azumi, wata kungiya mai zaman kanta ce mai suna Gidauniyar RAK ta shirya.

Khadijat wadda ta zama gwarzuwar musabakar a karamin mataki ta samu kyautar kudi N100,000 da sauran kayatattun kyaututtuka, yayin da Bushroh Sulaiman, mai shekaru 13 da ta zo ta biyu ta samu N50,000, sai kuma Abdulkarim isa mai kimanin shekaru 14 da ya zo na uku ya sami N30,000.

Kazalika, Sulaiman Abdulakeem wanda shi ne ya zama zakara a ajin kwararru na gasar shi ma ya sami kyautar N100,000.

Da yake jawabi yayin bikin rufe gasar, shugaban gidauniyar, Abubakar Ogunlende ya ce babban makasudin shirya ta shi ne domin a nuna cewa Musulunci addinin zaman lafiya ne, ta hanyar zakulo hazikan matasa domin su nuna bajintarsu a cikinta.

“Lokacin da muka saka gasar, mutum 100 ne suka karbi fom, 58 daga ciki kuma suka amince za su shiga, 18 daga cikinsu kuma suka taka rawar gani; yau kuma ga shi muna karrama shida daga cikinsu a matsayin zakarun ajin kwararru da na masu tasowa.

“Muna sa ran zuwa badi za mu samu karin mutane da za su yi tururuwa domin shigar ta, wannan somin-tabi ne kawai,” inji shi.

Ogunlende, wanda kuma shi ne Sarkin Addini na yankin na Badagry ya ce kyaututtukan kudaden an bayar da su ne kawai da nufin zaburar da matasan su biya kudaden makarantarsu kuma su taimaka wa iyayensu.

Shi kuwa Shugaban Sashen Koyar da Larabci na Kwalejin Adeniran Ogunsanya da ke Ijanikan a Legas, kira ya yi ga Musulmi da su dage wajen koyar da ’ya’yansu muhimancin karatu Al-Kur’ani, yana mai cewa abin takaici ne yadda a yanzu matasa ba sa damuwa da koyon ilimin addini da na Al-Kur’ani.

A cewarsa, ta hanyar koyon ilimin sanin addinin na Musulunci ne kawai duniya za ta zauna lafiya.