’Yar Sheikh Dahiru Bauchi, Amina ta zama Mai ba da Shawara ta Musamman kan Harkokin Almajirai da Karatun Tsangaya ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.
Sanarwar da sakataren gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya fitar ta ce gwamnan ya ya nada Hajiya Amina Dahiru Bauchi ne tare da wasa wasu mutum bakwai saboda rawar da za su taka wajen ciyar da jihar gaba a bangarori daban-daban.
Sanarwar mai dauke da Sanya hannun Babban Daraktan Yada Labarai na gidan gwamnatin Jihar Isma’ila Uba Misilli, ta ce sauran sabbin mashawartan gwamnan na musamman sun hada da AIG Zubairu Mu’azu Mai Ritaya a matsayin mai ba da shawara kan harkar tsaro.
Aishatu Adamu ita ce mashawarciya kan harkar zuba jari da shirya-shirye na musamman; sai Madam Finney David, a bangaren harkokin ta.
- JAMB: Yau za a fara rajistar jarabawar UTME 2024
- Gaza: Isra’ila ta kashe Palasdinawa 23,968 ta jikkata 60,582 a kwana 100
Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai Ritaya ACP Ibrahim Bappah a shi ne Babban Daraktan hukumar tsaron da gwamnatin jihar ta kirkiro na cikin (GOSTEC).
Ibrahim Saidu Umar, ya zama Babban Mai Taimaka wa Gwamna na 1 kan harkokin tsare-tsare, sai Yakubu Sarma, a bangaren ayyukan gamagari.