✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Rashidi Yekini ta kammala karatu a Ingila

Rashida ’yar marigayi shahararren xan kwallon Najeriya Rashidi Yekini a karshen makon jiya ne ta kammala karatun da take yi a Jami’ar Dumonfoute da ke…

Rashida ’yar marigayi shahararren xan kwallon Najeriya Rashidi Yekini a karshen makon jiya ne ta kammala karatun da take yi a Jami’ar Dumonfoute da ke Leicester City na Ingila.

Kamar yadda rahoto ya nuna, Rashidat ita ce ta biyu a jerin xaliban da suka fi nuna kwazo a Jami’ar inda ta fita da sakamako mai daraja ta biyu (Second Best Oberall Student).

Rashida dai ta yi karatu ne a fannin haxa fina-finai (Cinematography) kuma ita ce xaliba ta biyu a xaukacin Jami’ar da suka fi nuna kwazo.

Kimanin shekara biyar kenan da Rashida ta samu gurbin karatu a Jami’ar jim kaxan bayan mahaifinta Rashidi Yekini ya kwanta dama.

Kamar yadda rahoto ya nuna, waxansu na hannun daman marigayin ne suka xauki nauyin karatunta ganin yadda matsaloli suka dabaibaye iyalan mamacin =da hakan ta sa da yawa daga cikin iyalan suka shiga mawuyacin hali.

Idan za a tuna marigayi Rashidi Yekini shi ne xan kwallon Najeriya na farko da ya fara zura kwallo a raga a gasar cin kofin duniya a shekarar 1994.  A wasan, Najeriya ce ta lallasa Bulgariya da ci 3-0 kuma Rashidi ne ya fara jefa kwallon farko a raga.

A shekarar 1993 ce aka zabi Rashidi Yekini a matsayin Gwarzon xan kwallon Afirka (African Player of the Year) saboda kwazonsa.

Idan za a tuna a bara Shugaban Majalisar Dattjjai, Sanata Bukola Saraki ya tallafa wa iyalan Rashidi Yekini  inda ya ba mahaifiyarsu jari sannan ya yi wa gidanta kwaskwarima ta hanyar kawata gidan da kayan alatu.

A wancan lokaci Aminiya ta kawo labarin irin tallafin da Shugaban Majalisar Dattijan ya yi ga iyalan marigayi Rashidi ciki har da irin hotunan kwaskwarimar da ya yi wa gidan mahaifiyar da ya lalace.