Mamba a Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP, Sanata Joy Emordi ta sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Hakan na zuwa ne bayan kazancewar rikicin cikin gidan PDP ta kai ga saukar bakwai daga cikin jagororin jam’iyyar na kasa daga mukamansu a ranar Talata.
Daraktan Yada Labaran Shugaban Kwamitin Rikon APC, Mamman Mohammed ne ya sanar da dawowar Sanata Joy Emordi zuwa jam’iyyar a ranar Laraba a Abuja.
Ya ambato Sanata Joy Emordi tana cewa tana da yakini cewa cigaban Najeriya na tare da jam’iyyar APC wadda gwamnatinta ke gudanar da Najeriya cikin gaskiya tare da kokarin kyautata rayuwar al’ummomi na gaba.
“Ina ba ku tabbacin samun biyayyata da goyon bayana domin samun nasarar jam’iyyar nan.
“Gwamnatin Tarayya karkashin APC na shimfida ayyuka a yankin Kudu Maso Gabas wanda hakan ke kara jawo ’yan PDP zuwa cikinta,” a cewarta
A nashi jawabin, Shugaban Rikon jam’iyyar APC na Kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ce shigowar Sanata Emordi da wasu jiga-jigan ’yan siyar yankin Kudu Maso Gabas cikin APC zai kara kawo hadin kan kasa.
“Yankin Kudu Maso Gabas na da karfi a siyasance kuma yana da muhimmanci ga hadin kan kasa; tabbas wannan zai kara hada kan Najeriya,” inji shi.