Gwarzuwar ’yar kwallon Afirka ta 2014 da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya (U-20) mai suna Asisat Oshoala ta samu nasarar komawa sa kulob din Liberpool na mata da ke Ingila a karshen makon jiya bayan ta rattaba hannu.
’Yar shekara 20, Asisat ta canza sheka ne daga kulob din Ribers Angels na Najeriya zuwa gasar rukuni-rukuni na mata na Ingila don cigaba da fafatawa a can.
Tuni ’yar kwallon ta bayyana matukar farin cikinta a kan wannan nasara da ta samu. Ta ce “Na yi imanin zan hadu da hazikan mata da suka kware a harkar kwallo a can da hakan zai sa na samu gogewar da ta dace da ni a harkar kwallo.”
Shi ma kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta Liberpool, Matt Beard, ya bayyana farin cikinsa a kan canza shekar da Asisat Oshoala ta yi zuwa kulob din Liberpool na mata. “A gaskiya mun yi babban kamu kuma ko shakka babu ’yar kwallon za ta taimakawa kulob din mu wajen samun nasarori a kakar wasa ta bana”, a lokacin da yake hira da manema labarai.
Asisat ita ce ta samu nasarar lashe kyautar Gwarzuwar ’yar kwallo da kuma wacce ta fi yawan zura kwallaye a gasar cin kofin duniya na mata na ’yan kasa da shekara 20 da ya gudana a bara.
A yanzu ita ce mace ta farko da ta samu nasarar canza sheka zuwa Ingila don fafatawa a gasar rukuni-rukuni na mata a fadin Afirka, al’amarin da ya sa ta kafa sabon tarihi.