✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Hadeja

Wata Bahadeja ce ta je Makka har sau uku amma kawarta ba ta kiran ta da Hajiya sai dai ta kira ta da sunanta na…

Wata Bahadeja ce ta je Makka har sau uku amma kawarta ba ta kiran ta da Hajiya sai dai ta kira ta da sunanta na asali. Abin ya dame ta sai rannan ta yi wa kawar tata nasiha, ta ce mata: “Kin ga fa Arafata ukku, jifata ukku amma ba ki ce mani Hajiya, sai dai ki kira ni da ’Yar Hadeja. To, ki ji tsoron Allah, ki tuba ki daina. Kina halaka kanki ne ba ki sani ba, kada ki mutu ki ci wuta. Ke ba ki kirana da Hajiya, yanzu ranar gobe kiyama ina za ki da wannan zunubin?

Daga Amiru Isah Bakori, 07068147933