Laftanar Changfe Maigari daga Jihar Filato ta zama mace ta farko mai tuƙa jirgin saman Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya.
Da haka yankin Arewa, musamman ma Arewa Tsakiya ya kafa tarihin samar da mace ta farko matukiyar jirgin rundunar.
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya taya Laftanar Changfe murnar kafa wannan tarihi a rundunar tsaron Nijeriya inda ta zama kallabi tsakanin rawunna.
Ya ce wanna tarihi da Jihar Filato ta kafa tun bayan samar da rundunar a shekarar 1964 abun murna ne da ba za a taba mantawa ba.
- Babu sansanin Sojin Faransa a Maiduguri — Sojoji
- Majalisa ta bukaci sojoji su saki shugaban Miyetti Allah
A shekarar 2016 ne Changfe ta zama hafsan sojin ruwa ta Nijeriya mai mukamin Sub-Laftana, bayan an yaye daga makarantar kananan hafsoshin soji (NDA da ke Kaduna.
Daga nan aka tura ta sashen jiragen sama na rundunar a Hedikwatar Horarwa ta Rundunar da ke Ebube-Eleme da ke Jihar Ribas.