Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayar da umarnin bude hudu daga cikin iyakokin Najeriya na kan tudu nan take.
Iyakokin da aka bude su ne na Illela a Jihar Sakkwato; Maigatari Jihar Jigawa; Seme a Jihar Legsa; da Mfun a Jihar Kuros Riba.
- Rashin tsaro: Kungiyar Izala ta umarci limamai su yi Alkunut
- 2023: Yarima ya bayyana kudirin tsaya wa takara
- Abin da ya sa na tube Sanusi daga Sarautar Kano —Ganduje
“Shugaban Kasa ya amince da shawarar kwamitin da nake jagoranta tare da Ministan Kasuwanci da Zuba Jari; Harkokin Cikin Gida; Mashawarci Kan Tsaron Kasa da Shugaban Kwastam.
“An dora wa kwamitin alhalin nazari da bayar da shawara kan bude iyakokin Najeriya kuma Shugaban Kasa ya amince da shawarwarin da muka bayar”, inji Ministsar Kudi Zainab Ahmed.
Da take sanar da hakan bayan taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC), Ministar ta ce kafin ko zuwa ranar 31 ga watan Disamba za a bude ragowar iyakokin kasar da suka shafe wata 16 a rufe.
Sai dai ta ce haramcin da ke kan shigo da kayayyaki da suka hada da shinkafa, kayan tsuntsaye da sauransu zai ci gaba da aiki.
Najeriya ta dauki matakin rufe iyakonkinta na kan tudu ne a wani yunkuri dakile matsalar tsaro inda take zargin ana shigo da makamai da miyagun kwayoyi ta kan iyakokin na kan tudu.
Ta kuma kafa hujja da neman farfado da harkar noma domin samar da isasshen abinci a cikin gida a matsayin dalilin yin hakan.
Rufe iyakokin ya sha suka musamman yadda ake ganin ya durkusar da harkokin masu shigo da kayayyaki da sauran masu harkoki a kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.
Kasashen da ke makwabtaka da Najeriya sun jima suna rokon kasar ta bude iyakokin, amma gwamatin kasar ta ki, duk da yarjejeniyar AfCFTA yin harkokin kasuwanci taskanin kasashen Afirka da Najeriya ta sanya hannu a kai.