Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta yi karin Naira 34,000 da kuma N21,000 a kan farashin mita.
Karin Naira 23,00o ke nan NERC ta yi a lokaci guda a farashin mitar daga Naira N58,661.69 a safiyar Laraba, ta wata sanarwa da ta fitar.
- Kotun daukaka kara ta kori karar Peter Obi kan zaben Tinubu
- Kotu ta kori bukatar soke zaben Tinubu da Shettima
Sanarwar ta ce daga yanzu farashin mita mai amfani da layi uku ya karu zuwa N81,975.16k daga N58,661.69k.
Mita mai famni da layi uku kuma an kara kudinsa da Naira 34,000 daga N109,684.36kzuwa N143,836.10k .
Sanarwar da shugaban hukumar Sanusi Garba da Kwwamishinan Dafe Akpeneye, suka fitar sun sanar cewa karin ya dace da kamfanonin wutar lantarki da kuma masu amfani da ita.
“Zai ba wa kamfanoni damar saye da kuma gyaran mitocin da samar wa kwastomomi farashin da ya dace da su ba tare da tsawwala musu ba, a yanayin matsin tattalin arzikin da ake ciki a kasar,” in ji sanarwar.