Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya sa dokar ba-shiga ba-fita, ba-dare ba-rana a Yola babban birnin jihar sakamakon wasoson kayan tallafi da matasa suka yi.
Dokar da ya sanar ranar Lahadi ta fara aiki ne nan take.
Gwamnan ya ce hakan ya biyo bayan yadda matasan ke yawo da muggan makamai suna kai farmaki kan dukiyar al’umma a shaguna da gidaje.
Wani magidanci ya kashe saurayin matarsa a Adamawa
Gobarar Igiyar Leko ta yi ajalin Almajirai 3 a Adamawa
Kafa dokar na nufin babu wanda za a amince ya yi zirga-zirga a titunan jihar Adamawa sai waɗanda ke ayyuka na musamman.
Gwamna Fintiri ya kuma roƙi al’umma da mazauna jihar su yi biyayya ga dokar domin duk wanda ya saɓa za a kama shi domin gurfanarwa gaban shari’a.