Fitaccen dan Siyasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a Jamhuriyya ta biyu, Alhaji Balarabe Musa ya bayyana cewa sai barawo ne kawai zai iya zama shugaban kasa a Najeriya.
Tsohon Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da mai neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya, mawallafin Jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters, Mista Omoyele Sowore ya kai masa ziyara gidansa a Kaduna ranar Talatar da ta gabata.
Yana mai cewa “Babu wanda zai zama shugaban Najeriya sai dai idan shi barawo ne ko kuma barayi ne suke goya masa baya. Domin kusan kashi 99 cikin 100 na mutanen da ke rike da madafun ikon kasar nan duk barayi ne. Ta yaya mutum zai zama shugaban Najeriya in har bai fara zama barawo ba tukunna? Gaskiyar a bayyane take karara cewa, idan ba haka ba, waye zai iya kashe biliyoyin kudi a yakin neman zabe,” in ji Alhaji Balarabe.
To amma sai dai babu wata shaida da ya bayar da ta karfafa kalaman nasa. Alhaji Balarabe Musa ya ce sai dai a baya an samu shugabannin da suka yi mulkin kasar nan wadanda ba barayi ba, inda ya ba da misali da jamhuriyya ta biyu. “Ka ga Alhaji Shehu Shagari ya mulki Najeriya, kuma bai yi sata ba, amma a yanzu ba za a iya samun irin haka ba.”
Ya kuma kara da cewa dalilin da ya sa Najeriya ba ta samu ci gaban da ya kamata ba duk kuwa da irin dumbin arzikin da Allah Ya yi mata shi ne, rashin kyawawan tsare-tsaren tattalin arziki da na siyasa.
“A duk lokacin da aka kasa samun kyakkyawan tsari, to dole a samu kai a yanayin da Najeriya ke ciki a yau na bakin talauci da rashin hadin kai, duk kuwa da dumbin arzikinta. Kuma idan ba a yi hankali ba sai abun ya fi haka muni a nan gaba,” a cewarsa.
A cikin bayanin da Mista Sowore, ya bayyana cewa ya ziyarci tsohon gwamnan ne don neman shawarwarinsa game da al’amuran da ya sanya gaba na neman shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa na 2019. Ya jefa tambaya ga dattijon mai shekaru 81 cewa, menene ra’ayinsa game da yadda shugabannin baya suka gaza kai bantensu? Inda Balarabe Musa ya ce, “ba komai ne ya jefa kasar nan cikin halin da ta shiga ba face rashin tsarin siyasa mai kyau.
To amma da dan jaridar ya tambaye shi ko menene nagartar shugabancin Najeriya, Sai ya ce “Babban nagartar shugabancin Najeriya shi ne sata. Tun bayan rushewar Jamhuriya ta biyu a Najeriya, ka taba ganin wanda ya mulki kasar nan wanda ba barawo ba? Kodayake akwai ‘yan kalilan… Ba ina cewa dari bisa dari babu nagari ba, amma ina shakkar idan sun kai kashi 10 cikin 100, fiye da kashi 90 duk barayi ne, a cewar Alhaji Balarabe Musa.