✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanzu na fi son yin wakokin gambara – Fa’iza Badawa

Fa’iza Muhammad Badawa mawakiya ce wacce ta shafe shekara goma tana harkar waka, kama daga kan wakokin fim da na siyasa har zuwa na bikin…

Fa’iza Muhammad Badawa mawakiya ce wacce ta shafe shekara goma tana harkar waka, kama daga kan wakokin fim da na siyasa har zuwa na bikin aure da na sarauta. Sai dai a yanzu ta zo da wani sabon salo wanda ba a saba gani a wajen mawakan Hausa mata ba. A yanzu mawakiyar tana gudanar da wakokinta ne da salon gambara. A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana yadda aka yi ta fara amfani da wannan salo da kuma sauran batutuwa da suka shafi harkar waka:

 

Bari mu fara da jin tarihin rayuwarki, shin wace ce Fa’iza?

Sunana Fa’iza Muhammad, an haife ni a unguwar Badawa cikin Jihar Kano. A nan na yi makarantar firamare da sakandare dina. Daga nan kuma ban ci gaba da karatu ba sai na tsunduma cikin harkar waka ka’in da na’in.

 

Yaya aka yi kika fara waka?

Na fara harkar waka tun ina karama, domin na fara ne da

irin wakokin yabon Manzon Allah da ake yi a makaranatar  Islamiyya, musamamn a lokacin maulidi. A wancan lokaci yawanci malamai ke rubuta mana wakokinmu kuma mu rera. To a haka na taso na sami kaina  a cikin harkar waka. Ba zan iya cewa sha’awa ce ta kai ni na fara waka ba. Daga baya kuma kamar shekaru 10 da suka wuce sai na fara wakokin fim da na bikin aure da sauransu.

Wadanne irin wakoki kika fi yi?

Duk da cewa da farkon fara wakokina na fi yin wakokin fim amma a yanzu na fi yin wakokin siyasa da na bukukuwan aure da nadin sarauta da sauransu.

 

Zuwa yanzu wakoki nawa kika yi kuma wacce waka ce a ciki ta fito da ke?

Ba zan iya kirga yawan wakokin da na yi ba, domin a da na fara wannan lissafin amma daga baya lissafin ya rikice, don haka ba zan iya cewa ga adadin wakokina ba. Idan zan iya tunawa, wakar da zan iya cewa ita ta fito da ni, ita ce wata wakar fim mai suna dan Lukuti dan Siriri, wacce aka yi a fim din Oga Abuja, wanda Daso da marigayi Ibro suka yi. A wannan shekarar kuma zan iya cewa wakar da take tashe ita ce wacce muka yi da Sadik Zazzabi mai taken Ga Maza Bayanka, wacce muka yi wa tsohon Gwamna Kwankwaso.

 

Bayan wakokin da kika saba yi na yau da kullum, sai kuma aka ji ki kin fito da wani sabon salo a harkar wakarki, wato yanayin wakokin gambara. Ya aka yi hakan ta kasance?

Salon wakar gambara da nake yi, wani mai shirin fim ne ya nemi da na yi masa waka mai wannan salon. Da farko ma na nuna masa ba zan iya ba, amma sai ya dage cewa ni yake so na yi masa wakar. Hakan ya sa na amsa masa da cewa zan je na gwada. Daga nan sai na je na sami ire-iren wadannan wakoki na Hausa na saurare su, sannan sai na fito da nawa sabon salon, inda kuma na yi masa wakar ’Yar Gambara. Da yake ita wakar mutum biyu ke yinta, don haka sai na nemi taimakon Ado Gwanja muka yi wakar tare. A lokacin da aka yi wakar ban taba zaton za ta yi tashe ba, amma sai ga shi ta sami karbuwa don a loakcin ko’ina ka shiga za ka tarar wakar ake sauraro. To tun daga nan sai wannan waka ta ’yar Gambara ta bude hanya. Masu ba ni aiki musamman wakokin siyasa sai suka rika nuna sha’awarsu da wannan salon. Ni yanzu ma na fi son na yi wakokina da wannan salon, musamman wakokin siyasa, domin sun fi dadi. Kin san shi salon wakar gambara ana yin amfani da kalmomin zambo da habaici da sauransu. Hakan ya sa suka fi dacewa da jigon siyasa.

Wace irin matsala kika fuskanta lokacin da kika fara wakar Gambara, ma’ana akwai wahala a cikin wakar?

Babu wata matsala ko wahala da na fuskanta wajen yin wakar gambara, ina yin ta kamar yadda na saba sauran wakokina. Kamar yadda na gaya miki da farko, na nuna ba zan iya ba saboda ban taba yi ba amma da na ga wanda ya ba ni aikin ya dage a kan ni yake so na yi masa wakar, don haka sai na karfafa gwiwata cewa zan iya. Kuma cikin ikon Allah ban sami wata matsala ba. Na yi masa wakar kamar yadda yake bukata. Alhamdu lillahi, ni dama ina da karfin gwiwa, waka ba ta ba ni tsoro. A yanzu ka nemi na yi maka waka, to in sha Allah zan yi ta ba tare da tunanin faruwar wata matsala ba. Madogarata ita ce na san akwai wadanda suka fi ni iyawa amma ka zabe ni zan yi maka, don haka sai na karfafa gwiwata a kan hakan. Matsalar da zan iya cewa na fuskanta guda daya ce, kasancewar wakar ’Yar Gambara ta riga fim din fitowa, to sai wasu mutane suka rika zaton su nake yi wa zambo da habaici.

 

Waye gwaninki a mawakan Hausa?

A gaskiya ba ni da gwanin da ya wuce Mamman Shata. Haka kuma a mata na fi son wakokin Gwaggo Marka.

 

Wane kira kike da shi ga ’yan uwanki mawaka?

Ina kira gare mu da mu ci gaba da hada kai. Ni dai zan iya cewa a bangrena, ba ni da wani abokin gaba a cikin mawaka. Ina mu’amala da kowa daidai gwargwado. Idan abu ya taso mukan hada kai tare, zai yi wuya ma a yi waka ta gaba dayan mawaka ki ji babu muryata a ciki. Ina kira ga ’yan uwana mawaka, musamamn masu yin waokin yabon Annabi da su rika natsuwa wajen zaben kalmomin da suka dace. Ni ko wakokin siyasa na yi nakan ba wasu ’yan uwana mawaka su duba min domin yin gyaran da ya dace.

 

Wane sako kike da shi ga masoyanki masu sauraro?

Ina gaida masoyana tare da yi musu albishir cewa su saurari alabena dina mai fitowa. Dama ban taba yin alabe ba, wannan shi ne karo na farko da zan yi haka kuma wakokin za su zo a cikin hoton bidiyo ne duk da cewa ba ni zan fito a ciki ba kanwata ce Fatima amma muryata ce za ta rera wakokin.