✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanzu Dangote ne na 64 mafi yawan dukiya a duniya

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya samu ci gaba, inda a yanzu ya kasance attajiri na 64 mafi dukiya a duk duniya. A…

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya samu ci gaba, inda a yanzu ya kasance attajiri na 64 mafi dukiya a duk duniya. A halin yanzu an yi kirdaddon cewa Aliko Dangote ya mallakin Dalar Amurka biliyan 16 da miliyan 600, wanda hakan ya ba shi damar samun wannan kambi, domin kuwa a baya shi ne mutum na 103 a jerin attajiran duniya.

Aliko Dangote dai shi ne wanda ya fi kowa yawan dukiya a Nahiyar Afirka kuma tsawon shekara takwas ke nan yake rike da wannan kambin a nahiyar. A mujallar Bloomberg wadda ta fito a makon jiya, Alhaji Aliko Dangote ne kadai dan Najeriya da sunansa ya fito a jerin attajiran duniya 500 da mujallar ta wallafa. Wannan mujalla dai ana wallafa ta ce a kowace shekara.

Attajiri Jeff Bezos har yanzu shi ne mutum mafi yawan dukiya a duniya, inda aka yi ittifakin cewa ya mallaki Dalar Amurka biliyan 136. Shi kuma Bill Gates ya kasance mutum na biyu mafi yawan dukiya a duniya, a yayin da  attajiri Warren Buffet ya kasance mutum na uku a jerin attajiran duniya. A yayin da Bill Gates ke da Dalar Amurka biliyan 98.4, shi kuwa Warren ya mallaki Dalar Amurka biliyan 83 ne. Wannan ya kara tabbatar da cewa mutanen yankin Amurka ta Arewa su ne suka mamaye yawan attajiran da suka fi kowa yawan dukiya a duniya.

Kamar yadda binciken Mujallar Bloomberg ya tabbatar, dukiyar Dangote  kimarta ta dara wadda Mujallar Forbes ta ruwaito a baya. Mujallar ta Forbes, wacce take bayyana labaran hamshakan attajiran duniya, ta wallafa cewa Dangote ya mallaki Dalar Amurka biliyan 10.8 a kididdigar attajiran duniya da ta wallafa a fitowar mujallar a Janairun da ya gabata. Amma duk da haka, ita ma mujallar ta Forbes, ta kara tabbatar da cewa shi ne na daya a yawan dukiya a Afirka, matsayin da yake rike da shi a tsawon shekaru takwas zuwa yanzu.

A wannan jerin sunaye na attajiran duniya da Mujallar Bloomberg ta fitar a makon jiya, sunayen ’yan Afrika  biyar ne kadai suka bayyana, cikin attajirai 500 da aka gabatar.

Sunan Dangote ne ya kasance na farko a Afirka, sannan ya kasance na 64 a  duk fadin dniya.

Sauran attajirai hudu ’yan Afirka da sunayensu suka bayyana cikin lissafin sun hada da Nicky Oppenheimer dan kasar Afirka ta Kudu, wanda ya kasance attajiri na 216 mafi yawan dukiya a duniya. Ya mallaki Dalar Amurka biliyan 7.05. Sai kuma Johann Rupert, shi ma dan kasar Afirka ta Kudu, wanda ya kasance attajiri na 225 mafi yawan dukiya a duniya. Ya mallaki Dalar Amurka bilyan 6.92. Sai kuma Natie Kash, shi ma dan kasar Afirka ta Kudu, wanda ya kasance na 263 a jerin attajiran duniya. Ya mallaki Dalar Amurka biliyan 6.10.

Dan Afirka na biyar da sunansa ya fito a Mujallar Bloomberg a jerin hamshakan attajiran duniya, shi ne Naguib Sawiris dan kasar Masar, wanda shi ne attajiri na 331 mafi yawan dukiya a duniya. An kiyasta cewa ya mallaki Dalar Amurka biliyan 5.12.