✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yancin dan Adam, wanne kuma don me?

A want ton karon, Malama A’isha Usman Liman [email protected]  ce ta ziyarci Gizagawan Zumunci wannan muhimmiyar fadakarwa ga al’umma. Ga abin da malamar take cewa:Ya…

A want ton karon, Malama A’isha Usman Liman [email protected]  ce ta ziyarci Gizagawan Zumunci wannan muhimmiyar fadakarwa ga al’umma. Ga abin da malamar take cewa:
Ya kai mutum, ka sani Allah Ya ba ka dukkan ’yanci, domin Allah Yana da tsarinSa a kan komai da zai kasance.
Allah Ya halicci kakanmu Adam, Ya sa shi cikin aljannar dausayi kafin Ya kawo shi wannan duniya, kamar yadda Ya tsara zai kasance. Ya yi umurni a gare shi da kar ya ci wata bishiya, sai Iblis ya sanya waswasi zuwa gare shi, ya ce: “Ya Adamu, shin in shiryar da kai ga itaciyar dauwama a mulki wanda ba ya karewa?” Sai ya yaudare shi ya ci, sai Allah Ya turo su duniya, shi da matarsa Hauwa’u da kuma shi kansa Iblis din.
Adam da Hauwa’u ne kadai a doron wannan duniyar, sai dabbobi da tsirrai, wadanda tuni Allah Ya halicce su, Ya baza su ko’ina.
A haka suka rayu har suka fara haihuwa cikin kunci da takaici har sai da Allah Ya karbi tubansu, Ya aiko masu da shiriya. Daga wannan lokacin sai Allah Ya kalubalanci Adam da ’ya’yansa da bin shiriya irin taSa. Daga wannan umurni ne aka kafa tushen shari’a da hukunci, don sama wa kowanne dan Adam ’yanci cikin doron duniya. Gwagwarmaya tsakanin ayyukan alheri da na sharri ita ma ta kafa harsashinta – alheri dai shi ne na Allah, sharri ko shi ne na Iblis. Ya rage ga dan Adam ya zabi Allah  ko kuma ya zabi Iblis. Zabin Allah shi ne daidai.
A wannan filin na zabi tsakanin Allah ko Iblis sai Allah Ya samar wa dan Adam ‘yanci,’ watau kulle-kullen zuciyarsa; domin dan Adam ba shi da makamin yaki don ceton kansa ko cutar kansa, sai ’yancinsa.
Kodayake wannan ’yanci kuskure ya fara jawo wa Adam (a aljanna) amma kuma da shi ’yancin Adam da ’ya’yansa za su iya cetar kansu daga wannan kaucewa da suka yi daga kyakkyawar halitta mai tsarki, su koma kan hanyar da za ta maida su ga mahaliccinsu kamar yadda suke a da can.
Masu son bincike sa iya tambayar ‘me ya sa Allah Ya ba mu wannan ’yanci na zabi? Me ya sa bai bar mu kamar mala’iku marasa ’yanci ba, domin mu yi ta bin umarninsa kawai, har sai mun mutu? Me ya sa zai yi mana hisabi, ya hukunta mu idan mun aikata abubuwan da ’yancinmu ya raya mana mu aikata, alhali Shi ya ga damar ba mu ’yanci? Shin sharri ne a gare mu wannan ’yancin?
Duk wadannan tambayoyi a kan hanyar neman ilimi suke, suna neman bincike mai zurfi amma a takaice, ga amsoshinsu:
Da farko dai, ba wata amsa da za mu iya bayarwa mai ma’ana a takaice kan dalilin da ya sa Allah Ya halicce mu, illa mu ce, ‘don Ya ga dama.” Don Ya ga damar ne Ya sa kowace halitta ta bauta maSa, ko tana so ko ba ta so kuma a kan wannan tsarin ake; kawai sai abin da Allah Ya umurce su. Amma dan Adam sai Allah Ya sama masa ’yanci na hankali da lura da tunanin kansa da sanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Allah Ya riga Ya san shirin da Ya yi, komai zai koma ne gare Shi a karshen lokaci, domin Ya yi hukunci, sannan Ya saka masa daidai ayyukansa. Lallai ne ’ya’yan Adam su yi hankali da zabi a kan yadda za su gudanar da rayuwarsu, domin su ne za su zama masu daukar nauyin ayyukansu.
Lallai Allah cikin hikimarSa Ya ware halittunsa aji-aji. Ya ba da ’yanci daidai yadda ya ga Ya dace da wannan halittar. Daga halittar dan Adam (sabuwar halitta) sai Allah Ya ba shi kwakwalwa da zuciya mai tunani, sai ya hore masa ’yancin sarrafa su, domin samun ’yancin tafiyar da rayuwarsa cikin doron duniyarSa. Saboda Allah Ya san dan Adam zai yalwata cikin kabilu da Jinsuna da harsuna iri-iri a kasashe daban-daban kuma imaninsa da al’adunsa da muhallinsa da dangantakarsa da ci gabansa, duk za su bambanta daga kusurwa zuwa kusurwa na doron duniya.
Duk wadannan za su bukaci ’yanci da yadda za su sarrafu a zuciyar dan Adam ta hanyoyi masu yawan gaske a rayuwarsa. To amma da Allah Ya halicci ’yanci ya sa dama ce ta yin zabi kuma dan Adam zai iya zabar ya bi umurni ko ya ki bin umurni. Duk da munancin kin bin umurni, rashin wannan ’yanci tawaya ce, wadda za ta dusashe muhimmancin dan Adam, sannan ta illanci yadda Allah Ya tsara rayuwar dan Adam a duniya, domin khalifancin da Allah Ya turo dan Adam Ya yi a duniya ba zai tabbata ba idan ba shi da cikakken ’yancin kansa da yadda zai tafiyar da rayuwarsa yadda ta shafe shi, a inda yake tare da sarrafa baiwar da Ya yi masa don Ya khalifance Sa a doron kasa.
Lallai idan muka yi la’akari, za mu ga ashe rashin ’yanci ga dan Adam mummunan abu ne. To amma ya aka yi wannan rashin bai zama mummuna ga mala’iku ba? Amsa: Domin a kodayaushe suna gaban Allah kuma Ya riga Ya halicce su ta yadda umurninSa kawai za su iya aiwatarwa.
Ashe kuwa irin wannan ’yanci da Allah Ya ba Adam da ’ya’yansa, lallai baiwa ce a gare su, domin shi ne zai sa su ji dadin zama da zamantakewa a cikin wannan duniya mai cike da abubuwan so da na ki da abubuwan ban sha’awa da na ban haushi, danniya da adalci, sauki, da wahala da sauransu da dama.
dan Adam yana da ’yancin ya yi amfani da tunanisa ya zabar wa kansa tafarkin da zai bi, hagu ko dama – Dama dai ya san hanyar Allah ke nan (Alheri), Hagu kuwa hanyar shaidan (sharri). Ya rage wa ’yancinsa ya zabar masa amma dai dan Adam ya sani, alheri sakamakonsa alheri, sharri sakamakonshi sharri, ko a duniya ko a lahira. Wannan shi ne ’yancin da Allah Ya samar wa Adam da ’ya’yansa adoron kasa.
Tun daga lokacin da ’ya’yan Adam suka fara yaduwa ta hanyar haife-haife sai fafutuka ta son shugabanci da mulki ta kunno kai a tsakaninsu, ya kasance kowa yana son ya zama shi ne shugaba. To daga wannan takaddama ce suka fara samun matsaloli na rabuwar kawuna da keta da hassada da mugunta da zagon kasa da kyashi ga junansu. Daga wannan lokaci sai rarrabuwa ta fara, duk wanda ba zai samu shugabancin muhallin da yake ba sai ya fara tunanin ko dai ya tashi tsaye ya bayyanar da wadancan halayen (na kta, hassada, mugunta zagon kasa da kyashi) ko kuma ya yanke shawarar tattara iyalansa ya kara gaba can da nisa saboda yana ganin tunda ba zai yi mulki ba, to shi ma ba za a mulke shi ba. A haka ana warewa har aka samar da unguwanni, garuruwa, kasashe, har duniya ta kasance yadda take a yanzu. Amma duk da haka duk inda mutane suka fara taruwa, to daga nan sai takaddama ta soma tashi, don fafutukar neman shugabanci. Irin wannan yanayin ne ya samar da yanayin fitintinu da tashe-tashen hankula a duniya, har daga bisani sai ’ya’yan Adam na wancan lokutan suka sami dubarar a kaddamar da wata gasar fada ta neman fin karfi, duk wanda ya fi karfi to shi ne shugaba, wanda kuma aka fi shi karfi shi ne mai biya. Daga nan sai abin ya fara yaduwa daga wannan unguwa zuwa waccan. Haka abin yake a kauye ko gari, mai nasara shi ne shugaba ga wanda bai yi nasara ba.
Za mu ci gaba