✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanayin zafi ya karu bayan ruwan sama na farko a Abuja

Wasu mazauna birnin Abuja da kewaye sun bayyana karuwar yanayin zafi a birnin biyo bayan ruwan sama daya da aka yi a ranar Lahadi. Karon…

Wasu mazauna birnin Abuja da kewaye sun bayyana karuwar yanayin zafi a birnin biyo bayan ruwan sama daya da aka yi a ranar Lahadi.

Karon farko kenan da aka samu ruwa a shirye-shiryen shiga damunar bana.

An samu saukan ruwan ne a gundumomin Jabi, Utako da Maitama, duk a babban birnin.

Wasu mazauna birnin da suka tattauna da Aminiya, sun bayyana yadda zafi ya karu a birnin bayan da ruwan ya gama sauka.

Margret Ben, ta ce tayi matukar murna da samun ruwan, amma kuma ta koka da cewa ruwan baiyi yawan da zai sassauta yanayin zafin da ake ciki a birnin ba.

“Ruwan farko a bana ya kawo matukar zafi fiye da yadda ake tunani. Har yanzu gumi nake yi saboda zafi duk da cewa ruwan sama ya sauka.”

A nashi bangaren, wani mazaunin birnin mai suna, Sunday Jonah Abah, ya ce “Mun godewa Allah da ya nuna mana sabon yanayi. Yanayin zafin garin kuma ya karu duk da cewa an yi ruwan sama.”

Comfort Pem, ta ce “Yanayin ba shi da dadi. Da naga an fara ruwa, na dauka za’a samu yanayi mai sauki, amma gaskiya yanayin zafin karuwa ya yi.”