’Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Kaduna da ke hannun ’yan bindiga sun gudanar da zanga-zanga a Hedikwatar Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto dai ma’aikatanw wannan ma’aikata ba su samu damar shiga ofisoshinsu ba saboda masu zanga-zangar sun toshe hanyoyin.
- Yadda hana biyan fansa ya jawo bidiyon dukan fasinjojin jirgin kasa
- Ana zaben neman kara wa shugaban kasa Karfin iko a Tunisiya
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan bullar bidiyon dukan fasinjojin da ’yan bindigar su ka yi, tare da barazanar sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, bisa kin biya musu bukatunsu.
Bullar bidiyon dai ta daga hankalin ’yan uwan fasinjojin da kuma da dama daga cikin ’yan Najeriya.
Hakan ne ma ya sa su fita zanga-zanagar a safiyar ranar Litnin din zuwa ma’aikatar da ke kula da sufurin jirgin kasan Najeriya.
Aminiya ta gano masu zanga-zangar suna dauke da takardu masu rubuce-rubucen bukatar karbo musu ’yan uwansu daga hannun ’yan ta’addan.
Wata majiya ta bayyana mana cewa dakile masu kai kudaden fansar mutanen da aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ne ya sanya ’yan bindigar yi wa fasinjojin da ke hannunsu dukan tsiya, da kuma bacin rai ga ”yan uwan.