✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Tijjaniya a Kudu sun yi wa Halifa Sanusi II mubaya’a

Zai tabbatar da hadin kan ’yan Darikar Tijjaniya mai muridai fiye da miliyan 70 a Najeriya.

Halifan Tijjaniya a Najeriya, Halifa Muhammadu Sanusi II ya gana da halifofi da mukaddamai da daruruwan muridai da suka fito daga jihohi shida na Kudu maso Yamma.

Haka kuma, ya gana da mabiyan darikar a jihohi biyu na Kudu maso Kudu da Jihar Kwara, inda ya tabbatar da burinsa na sake fasalin Darikar Tijjaniya, musamman wajen samar da hadin kai da kyautata zamantakewa a tsakaninsu da sauran mutanen Najeriya.

Halifa Sanusi II da ayarinsa sun ziyarci birnin Ibadan ne a makon da ya gabata inda suka yi ganawa a karon farko da halifofin yankunan.

Ya shaida musu cewa muhimmin abin da ya sanya a gaba tun daga lokacin da aka tabbatar masa da Halifancin Tijjaniya a Najeriya shi ne hadin kan ’yan Darikar Tijjaniya mai muridai fiye da miliyan 70 a Najeriya.

Ya ce zai lalubo hanyar inganta ilimin addini da na zamani ga kananan yara domin sanin addininsu da ainihin ilimin Darikar Tijjaniya domin zama manyan gobe.

Kazalika, ya ce zai yi fafutikar samar da ayyukan yi da sana’o’i ga matasa da kyautata zamantakewa a tsakanin Musumi da mabiya wasu addinai da tabbatar da kishin kasa domin kawar da bambancin kabila da bangaranci.

A ranar farko da Halifa Sanusi II ya sauka a Ibadan ya wuce kai-tsaye ne zuwa Babban Masallacin Shamsu-Sahood da ke Unguwar Orita-Aperin inda ya jagoranci dubban Musulmi a Sallar Juma’a.

Ayarin ya ziyarci kabarin Sheikh Sani Awwal da ke Madina Elekuro wanda shi ne wakilin Sheikh Ibrahim Nyas na farko a Kudu maso Yamma.

Daga bisani ya kai ziyarar ban girma a fadar Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji.

Haka kuma ya ziyarci Babban Masallacin Unguwar Sabo Ibadan, inda ya jagoranci dimbin Musulmi mabiya Darikar Tijjaniya yin Zikirin Juma’a tare da jagorantar sallolin Magriba da Isha’i kafin ya wuce zuwa masaukinsa.

A rana ta biyu da Halifa Sanusi II ya gana da halifofi da mukaddamai a masaukinsa kafin su wuce gidan gwamnati domin gaisuwar ban girma ga Gwamna Seyi Makinde wanda shi ne ya bukaci a kai masa ziyarar.

Dukkan halifofi da mukaddamai da muridai na yankin sun yi mubaya’a ga Halifa Muhammadu Sanusi II kamar yadda jagoran Darikar Tijjaniya a sashin Halifa Sheikh Salisu Alao Adenikan ya yi bayani.