✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan takarar shugaban kasa 12 sun taya Buhari murna

‘Yan takarar shugaban kasar Najeriya 12 da suka fadi zaben da aka yi ranar 23 ga Fabrairu 2019  sun taya shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar…

‘Yan takarar shugaban kasar Najeriya 12 da suka fadi zaben da aka yi ranar 23 ga Fabrairu 2019  sun taya shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC murnar lashe zaben shugaban Najeriya a karo na biyu.

Rukunin ‘yan takarar sun ce, shugaba Buhari ya cancanci lashe zaben da aka yi.

Shugaban rukunin da ‘yan takarar Mista Shittu Kabir ya ce, duk da yake akwai ‘yan takarar shugaban kasa da yawa amma daya kadai zai samu nasara kuma shi zai jagoranci kasar.