✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan ta’addan Birnin Gwari sun kona motar ’Yan Sanda

A ranar Litinin din nan ne wasu da ake zaton ’yan ta’addan Birnin Gwari ne, suka kaiwa wata motar ‘Yan Sanda (Excort) hari har suka…

A ranar Litinin din nan ne wasu da ake zaton ’yan ta’addan Birnin Gwari ne, suka kaiwa wata motar ‘Yan Sanda (Excort) hari har suka konata akan hanyar Udawa zuwa Kaduna.

Majiyar mu a yankin ta shaidawa Aminiya cewa, yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 12 na rana a lokacin da motar ke kan hanyarta na zuwa Kaduna .

A cewar majiyar mu, harin ya faru ne a kusa da wani guri da ake kira Kwaru kusa da garin Udawa.‎ Kuma motar kirar Hilux ce aka kona.

Majiyar tamu wanda yana daga cikin ‘yan bangan yankin na Udawa ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun harbi Dan Sanda daya a cikin motar amma bai rasu ba, an kaishi asibiti don masa magani.

Har ila yau, ya ce a lokacin artabun da aka yi akwai dan banga daya da shima ya samu raunin harbi  kuma shima yana amsar magani a wani asibiti.