✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun tsere daga gidan yarin Nijar

Fursunoni da dama sun tsere daga gidan yarin garin garin Koutoukale inda ake tsare da manyan mayakan jihadi

Manyan ’yan ta’adda sun tsere daga babban gidan yarin garin Koutoukale a Jihar Tillabery da ke Jamhuriyar Nijar.

Hukumomin Nijar sun ayyana dokar hana zirga-zirag a fadin Jihar Tillabery sakamakokn tserewar fursunonin.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan kasar ta tabbatar da tserewar fursunoni da dama ciki har da manyan ’yan ta’adda daga gidan yarin.

A ranar Alhamis da fare ne fursunonin suka tsere bayan fasa gidan yarin da ke garin Koutoukale mai nisan kilomita 50 daga binin Niamey.

A baya a sau biyu a shekarun 2016 da 2019 fursunoni sun yi yunkuri tserewa daga gidan yarin amma jami’an tsaro na dakile su.