Akalla mutum 17 ne suka rasu, wasu da dama kuma suka jikkata a harin da ’yan bindiga suka kai wani wurin hakar ma’adanai da ke karkashin kulawar wasu ’yan kasar China a yankin Gurman da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.
Harin da aka kai ranar Laraba a lokacin da wasu mutum bakwai ciki har da wasu ’yan sanda da ke aikin gadi, ya yi sanadiyar rasuwarsu duka.
- Atiku ya yi raddi ga masu sukar sa kan kin daukar Wike a matsayin mataimaki
- Gani ya kori Ji: Yadda ’yan Kannywood ke atisayen wasan Sarauniyar Zazzau
Maharan dai rahotanni na nuna suna dauke da muggan makamai, kuma sun dira a yankin ne da rana, suka nufi wurin tare da bude wa mutanen da ke gurin wuta.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyukan Jinkai na Jihar Neja, Emmanuel Umar, ya ce ya zuwa yanzu ba su tabbatar da adadin wadanda lamarin ya ritsa da su ba tukun.
Ya ce: “Sakamakon kiran gaggawa da muka samu ranar 29/6/2022 da misalin karfe 4 na yamma cewa ’yan bindiga sun kai hari wurin hakar ma’adinai da ke kauyen Ajata-Aboki da ke yankin Erena a Karamar hukumar Shiroro, sai muka tada jami’an tsaron hadin guiwa zuwa can domin agaza wa wadanda lamarin ya rutsa da su.”
Ya ce cikin wadanda iftila’in ya afka wa har da wasu ’yan kasar China hudu da ’yan bindigar suka sace.
“Jami’an tsaro sun tada runduna domin farauto sauran ’yan ta’addan tare da ceto wadanda suka jikkata, wadanda a cikinsu har da jami’an tsaronmu na hadin guiwa da suka samu raunuka daban-daban kuma yanzu haka suna asibitin ana yi musu magani.