Akalla mutum 12 ne suka rasu a wata musayar wuta da aka samu tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan sa-kai a kauyen Zak da ke Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
Garin na Zak dai yana da nisan kilomita 40 daga Wase, hedkwatar Karamar Hukumar ta Wase.
- Shin da gaske cin naman rakumi na karya Alwala?
- ’Yan Legas na cin abincin Naira biliyan 4 da rabi a kullum – Sanwo-Olu
Wani jami’in sa kai kuma Shugaban matasa a kauyen, Shapi’i Sambo, ya shaida mana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safiyar Lahadi, kuma ‘yan bindiga tara da jami’an sa-kai uku sun rasu sakamakon musayar wutar.
Kakakin rundunar tsaro ta Operation Safe Heaven, Manjo Ishaku Takwa, ya ce ya zuwa yanzu ba su tabbatar da adadin wadanda suka rasu ba sakamakon musayar wutar.
Kazalika ya ce rundunar ta dakile harin, sannan ta zarce kauyen Gajin domin ci gaba da yaki da ‘yan ta’addan da suka shiga yankin.
Idan za a iya tunawa dai a kwanakin baya, ‘yan bindigar sun ba wa mazauna kauyukan Sabon Zama da Gindin Dutse da Anguwan Tsohon Soja, da na Anguwan Mangu, duka a Karamar Hukumar ta Wase, wa’adin barin kauyukan ko su fuskanci fushin su.
Hakan dai ya razana da dama daga cikin mazauna kauyukan, inda suka kwashe kayansu suka gudu birane da kauyukan da ba sa jerin wadanda ‘yan bindigar suka aika wa gargadin.