✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan ta’adda sun kashe sojoji 11 a Syria

Sojoji 11 ne suka rasa rayukansu a hare-haren kungiyar ’yan ta’addan Tahri al-shamam kan yankin Arewa maso yammacin Syria ranar Laraba. Kungiyar kare hakkin dan…

Sojoji 11 ne suka rasa rayukansu a hare-haren kungiyar ’yan ta’addan Tahri al-shamam kan yankin Arewa maso yammacin Syria ranar Laraba.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Syria mai shalkwata a Birtaniya ta ce kungiyar ta harba roka da bama-bamai kan sansanin sojojin da ke Kafr Ruma , inda takwas da ke kusa da lardin Idlib  suka rasu.

Rahoton ya ce daga baya ne ’yan ta’addan suka harbe karin sojoji uku a kusa da yankin Kafr Nahl da shi ma ke lardin.

Yan ta’addan dai sun mamaye fiye da rabin yankin Idlib da sauran kewayen iyakar lardunan Aleppo, Hama da kuma Latakia.

Rahotanni na nuna fiye da rabin mutane miliyan uku da ke yankin sun rasa muhallansu dalilin hare-haren ’yan ta’addan.