✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sintiri na da gudunmuwa da za su ba da wajen samar da tsaro a Najeriya – Garba Juji

Alhaji Garba Juji shi ne Mataimakin Kwamandan Rundunar  kungiyar ‘Yan Sintiri  shiyar  Arewa  ta Tsakiya. Da yake zantawa da Aminiya a makon jiya, ya bayyana…

Alhaji Garba Juji shi ne Mataimakin Kwamandan Rundunar  kungiyar ‘Yan Sintiri  shiyar  Arewa  ta Tsakiya. Da yake zantawa da Aminiya a makon jiya, ya bayyana tarihin kungiyar ‘yan sintiri da  kuma irin gudunmawar da kungiyar ke ba da wa wajen magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasar nan da sauran su. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ko za ka bayyana mana tarihin wannan kungiyar?
An kafa wannan kungiyar ne a kasar nan a shekarar 1983 a garin Kaduna. Ganin cewa  akwai irin wannan kungiyar  a kusan dukkannin jihohin kasar nan, ya sanya  aka hada kai aka  yanke shawarar kafa wannan kungiya a matsayin kungiya ta kasa baki daya. Kuma an kafa ta ne don taimakon al’umma da rikon amanarsu. An mata rigistar da gwamnati a shekarar 1999. Tun lokacin da muka kafa ta,  mun  zauna ne a gidan Arewa da ke Kaduna, karkashin iyayen  wannan kungiyar wato  Alhaji Ali Sakkwato da Alhaji Bawa Garba (ABG) da Alhaji Ahmadu Chanchangi da Raji Rasaki Sarkin al’ummar Yarbawa mazauna Kaduna da Alhaji Sabo Maiduguri da sauransu. Daga nan ne muka  yanke shawarar cewa ya kamata wannan kungiyar ta fita daga cikin kungiyar ‘yan banga, domin ‘yan siyasa sun fara amfani da ‘yan banga wajen cimma burinsu na siyasa. A wannan lokaci ne aka cire wannan suna na banga zuwa kungiyar ‘yan sintiri ta Nijeriya.
Kamar wadanne jihohi ne kungiyarku ke da ofisoshi zuwa yanzu?
A yanzu mun bude ofisoshin wannan kungiya a duka jihohi 36 da ke fadin kasar nan da Babban Birnin Tarayya Abuja. Kuma a kalla muna da membobi sama da dubu 376 a baki dayan kasar nan.
Ganin irin matsalar rashin tsaron da ake fama da ita, wane irin gudunmawa ne wannan kungiya take bayarwa wajen magance wannan matsalar?
To, mun gode wa Allah duk cewa kungiyarmu na cikin  matsalar  rashin ababan hawa da sauran kayayyakin aiki, amma cikin yardar Ubangiji akwai gagarumar gudunmawar da muke bayarwa kan magance matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar nan. Domin da zarar mun ga wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiyar al’umma, idan wanda zamu kama ne mukan kama, idan kuma wanda zamu sanar da jami’an tsaro ne mukan sanar da su nan take.
Misali kamar irin abubuwan da suke faruwa a shiyar gabashin kasar nan wato yankin da al’ummar Ibo ke da rinjaye, ’yan kungiyarmu na yin aiki sosai don taimakawa wajen samar da tsaro a jihohi kamar su: Enugu da Anambra da Abiya da sauransu.
Hakazalika, a jihohin Legas da Ondo da Ibadan da Ekiti da Ogun da Osun.  Labarin ayyukan kungiyar haka yake a yankin arewacin kasar nan.
Ya kamata a fahimci irin girman gudunmuwar da muke ba da wa saboda mu ne muke cikin mutane don haka akwai abubuwan da zamu sani fiye da jami’an tsaro.
Wadanne irin nasarori ne kake ganin cewa wannan kungiya ta cimma zuwa yanzu?
Nasara ta farko dai da muka samu  ita ce mun sami nasarar hada kan ‘yan Nijeriya. Mun kawar da maganar addini da kabilanci tsakankanin membobin wannan kungiyar. Duk inda dan wannan kungiyar yake idan ya ga dan’uwansa da irin wannan kaki nan take zai rungume shi kamar ya ga dan uwansa na jini. Idan Ibo dan kungiyar sintiri  ya ga bahaushe dan kungiyar sintiri sanye da kaki zai karbe shi hannu bibbiyu. Duk inda muka tafi, idan ka ganmu, kanmu a hade  yake.
Sannan kuma maganar rashin tsaro muna bada gudunmawa a aikace muna bada gudunmawa da bayanai da kuma shawarwari. Wadannan kadan ne daga cikin nasarorin da muka samu.
Ta wace hanya kuke bi wajen raba wannan kungiyar da bata gari?
Muna da fom da muke bayar ga dukkan mai sha’awar shiga wannan kungiyar don cikewa kafin mutum ya zama dan wannan kungiyar. Wannan matakin ya taimaka sosai wajen raba ta bata gari. Saboda wanda yake sara suka, ko baraho ba zai shiga wannan kungiyar ba.
Don haka da zarar mun baiwa mutum fom din nan sai ya koma unguwarsu wajen mai unguwa da dittawan unguwar wadanda za su sanya masa hannu. Da wannan fom din ne muke tace mutanen da muke dauka a wannan kungiyar. Bayan wannan  kuma  muna da kwamitocin da suke tantance wadanda za mu
dauka, suna nan suna zaga wa unguwa-unguwa a fadin kasar nan. Idan mutum ya cika fom din da muka bashi, sai mu baiwa wadannan kwamitoci su duba su tantance. Ta wadannan hanyoyin ne muke tsare wannan kungiyar daga bata gari.
Kana da wani kira ko sako zuwa ga gwamnati da sauran jama’a?
Da farko muna kira ga gwamnatin tarayya karkashin Shugaban kasa Goodluck Jonathan kan ya taimaki kungiyar ‘yan sintiri. A tallafawa ‘yan wannan kungiya domin su rika cin gajiyar irin ayyukan da suke yi ta hanyar yanka masu wani albashi ko da kankani ne.
Kamar yadda aka wa wasu kungiyoyi. Kuma a tallafa mana da motoci da kuma sauran kayayyakin aiki.
Bayan haka, ina kira ga membobin wannan kungiyar da su ji tsoron Ubangiji duk abin da zasu yi suyi tsakani da Allah domin babban nauyin da ke kanmu.Babu maganar bambancin addini ko kabila, mu wa kowa adalci da ya dace. Mu tsaya wa gaskiya, mu guje wa cin-hanci da karbar rashawa.