✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Sibiliyan JTF 103 sun zama sojoji a Borno

Bisa la’akari da irin gudunmowar da matasa ‘yan-kato-da-gora suka bayar ta hanyar bai wa jami’an tsaro hadin kai wajen dakile  ayyukan ta’addancin Boko Haram da …

Bisa la’akari da irin gudunmowar da matasa ‘yan-kato-da-gora suka bayar ta hanyar bai wa jami’an tsaro hadin kai wajen dakile  ayyukan ta’addancin Boko Haram da  ya yi sanadiyyar lakume dimbin rayuka da dukiyoyin al’umma tun a shekarar 2009, Gwamnatin Jihar Borno a karkashin jagorancin Alhaji Kashim Shettima ta samar wa matasan na Sibilyan JTF 103 aikin soja, wadanda suke karbar horo yanzu haka a Zariya,  sannan ta yi alkawarin ci  gaba da tallafa masu ta kowace fuska, ta yadda za su ci gaba da taimaka wa al’ummarsu.

Da yake jawabi ga matasan su 103 wanda a yanzu haka suna samun horon aikin soja ne a Barikin Sojoji ta Depot dake Zariya, a yayin da suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa dake Maiduguri a cikin makon nan.

Gwamna Kashim ya kara da cewar “Ko shakka babu Sibiliyan JTF, ko kuma ‘yan gora sun taka rawar gani wajen cimma nasarar yakar Boko Haram har zuwa wannan lokacin, musanman yadda kuka hada hannu da jami’an tsaro tare da ba su bayanan sirri don kawo karshen lamarin, a haka zamu iya cewar kun sadaukar da rayuwarku saboda kare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu.”

“Kuma kun yi haka ne don kare wanzuwar kasarmu, don haka ba zamu taba mantawa da ku ba, zamu yi iya kokarinmu wajen inganta rayuwarku wanda shi ya sanya ma muka yanke shawarar samar maku da wannan aiki na soja tare kuma da kula da daukacin iyayenku,” a cewar Gwamna Shettima.

Daya daga cikin matasan wanda ya zama karamin soja da a yanzu da ya ki yarda a bayyana sunansa, ya ce “Babu ko shakka a yanzu ban yi da na sani ba wajen sanya kaina cikin wannan kungiya ta ‘yan-kato-da-gora ba, domin kuwa na ga ribarsa a yanzu, duk da cewar Boko Haram sun mayar da ni maraya don sun kashe mini iyaye.

“Kuma a dalilin hakan ne ma na dauki gora don yin ramakon gayya, wanda kuma a yanzu haka na yi ramakon gayyan, sannan kuma na sami aikin yi, baya ga sanina da wasu manyan mutane suka yi, kuma yanzu zan iya rike kaina da iyalina da wannan aiki na sojan da na samu, kuma za mu ci gaba da yakar Boko Haram a duk inda suke daga nan har zuwa karshen rayuwata. Ssannan kuma zan nemi a bar ni a Borno idan mun kammala koyon aikin Soja a Zariya, na kuma gode wa Gwamnatin Borno a karkashin jagorancin Gwamna Kashim Shettima,” inji shi.