’Yan sanda a Jihar Kano sun gayyaci tsohon Kwamishinan Ayyuka a Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, Injiniya Mu’az Magaji.
Mu’az, wanda Gwamnan ya kora bisa zargin ‘yin murna’ da rasuwar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, marigayi Abba Kyari, dai ya yi kaurin suna wajen caccakar Gwamnatin Ganduje.
- Babban taro: Rikici ya yi awon gaba da kujerar shugaban kungiyar Gwamnonin APC
- A watan Maris ’yan mata za su koma makaranta a Afghanistan – Taliban
Yana dai yawan sukar salon mulkin Gwamnan, da yadda iyalansa suke shiga harkokin mulkin Jihar kane- kane.
Tsohon Kwamishinan dai ya ce rundunar ’yan sandan ta kira shi ne ta waya, sannan ta umarce shi da ya bayyana a hedkwatarta da ke Kano don ya amsa wasu tambayoyi.
Ya ce gayyatar ba ta rasa nasaba da yawan sukar lamirin Gwamna Gandujen da yake yi.
Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da gayyatar, inda ya ce sun yi hakan ne bayan wani korafi da aka shigar a kansa.