✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Zamfara

’Yan bindiga sama da 100 sun kwashi kashinsu a hannun ’yan sanda a hanyar Gusau-Funtua

’Yan sanda a Jihar Zamfara sun yi luguden wuta  kan wasu ’yan bindiga sama da 100 da suka yi yunkurin kai farmaki a kan hanyar Gusau-Tsafe-Funtua.

Rundunar ’Yan Sanda Jihar Zamfara ta ce luguden wuta da jami’anta suka yi wa ’yan bindigar da suka tsare hanyar da nufin yin fashi ya sa maharan arcewa suka bar baburansu.

“Bayan samun rahot sai DPO na Tsafe ya jagoranci tawagar hadin gwiwar ’yan sanda zuwa wurin da aka tare hanyar.

“Bayan an yi dauki ba dadi, ’yan bindigar sun ranta a na ta zuwa cikin daji da raunukan bindiga yayin da suka bar baburansu 14 da wasu jakuna dauke da kayan sojoij,” inji Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Abutu Yaro.

Kwamishinan ’Yan Sandan ya ce a Sahen Bincikin Manyan Lafuka (CID) na gudanar da bincike, yayin da Rundunar ke ci gaba da matsa kaimi a kokarinta na ganin ta cafko ’yan bindigar da suka tsare.