✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun yi wa dan takarar Gwamnan Zamfara tambayoyi kan bata sunan Magajin Garin Sakkwato

Rundunar ’yan sanda mai gudanar da ayyuka sa ido na musamman dake karkashin ofishin shugaban ’yan sanda na kasa ta yi ma dan takarar gwamnan…

Rundunar ’yan sanda mai gudanar da ayyuka sa ido na musamman dake karkashin ofishin shugaban ’yan sanda na kasa ta yi ma dan takarar gwamnan Jihar Zamfara na Jam’iyyar APGA a zaben da ya gabata na 2019, Sani Abdullahi Shinkafi tambayoyi akan zargin da ake yi masa na bata suna da ya yi ma Magaji Garin Sakkwato, Alhaji Hassan Ahmad Danbaba.

Dan siyasar ya amsa tambayoyin ne a Hedikwatar ’Yan sanda ta kasa dake Abuja a ranar talatar da ta gabata, kamin daga baya a tsare shi a ofishin ’yan sanda dake Maitama.

Tun da fari Hukumar ’yan sanda ta kasa ta gayyaci Shinkafin ne ta hanyar aika masa da takardar gayyata wacce jami’i mai shugabantar rundunar ta musamman, Maitaikin Kwamishinan ’Yan sanda A. A. Elleman ya sanya ma hannu a ranar 16 ga watan Okutoba.

Shinkafi wanda shi ne shugaban riko na Kwamitin kwato kaddarorin Jihar Zamfara ya gurfana tare da amsa tambayoyin ’Yan sanda a gaban rundunar ta sa ido ta musamman ta shugaban ’yan sanda na kasa a ranar Litinin 21, ga watan Okutoba, 2019 da misalign karfe 10 na safe.

Takardar da aka aika masa dai tana bayanin cewa; “wannan ofishin yana bincike laifin bata suna da kuma karya, laifukan da aka kawo kokensu ga ofishin shugaban ’Yan sanda na kasa wanda kuma aka danganta da sunanka.

“Don haka, ana bukatarka da ka zo ka gabatar da kanka ga SP Usman Garba a ranar Litinin 21 ga watan Okutoba don ka amsa tambayoyi tare da yin karin bayani a game da zargin da ake yi maka.

“Bada hadin kanka yana da matukar muhimmanci a gare mu.”

Shinkafi ya rubuta wata budaddiyar wasika wacce a ranar 30 ga watan Satumba 2019, wacce a ciki ya yi ikirarin cewa ‘Magajin Garin Sakkwato ya mallake gidan saukar baki mallakar Jihar Zamfara dake Abuja mai suna Halal Hotal.

Ya kuma zaigi tsohon gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari da ‘zambatar jihar ta hanyar mika hotal din ga Alhaji Hassan Danbaba, tare kuma da zargin cewa hotal din yana samar da kudaden shiga da suka kai naira miliyan N950, 000, 000 a cikin shekaru takwas ‘ba tare da a sanya ko sisi a lalitar Jihar Zamfara.”

A nasa baryin Magajin Garin Sakkwato, ya karyata wadannan zargi inda ya ce Kamfaninsa ya karbi hayar hotal din ne na tsawon shekaru 25, kuma an bashi hayar ne a cikin 2009 a lokacin mulkin Gwamna Mahmuda Aliyu Shinkafi, kusan shekaru uku baya tun kafin Yari yah au gadon mulki. Don haka ne Alhaji Danbaba ya kai koken Shinkafi akan ya bata masa suna tare da yi masa kazafi.

Majiyarmu ta habaito mana cewa Shinkafi ya isa Hedikwatar ’yan sanda ne da misali karfe 12 na ranar Talata, inda kuma suka ci gaba da bincikensa. Daga baya an tsare shi a ofishin ’Yan sanda na Maitama har zuwa karfe 10 na daren wannan ranar. An bayar da belin Shinkafi bayan da wani tsohon shugaban ’Yan sanda daga Jihar Zamfara ya tsaya masa. ’Yan sanda sun bayyana cewa za su gabatar da shi a gaban Kotu da zarar sun kammala bincike.