✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun watsa masu zanga-zanga a Kaduna

’Yan sanda a Jihar Kaduna sun watsa taron masu zanga-zangar nuna alhinin kashe-kashe da ake yi a Kudancin Jihar. ’Yan sandan dauke da makamai sun tayar…

Yan sanda a Jihar Kaduna sun watsa taron masu zanga-zangar nuna alhinin kashe-kashe da ake yi a Kudancin Jihar.

’Yan sandan dauke da makamai sun tayar da taron ne a safiyar Asabar kafin wanda suka shirya shi su gama taruwa a mahadar Refinery Junction.

Kakakin ’yan sandan jihar, Mohammed Jagile ya ce, “Ba a sanar da mu ba. Mun je mun watsa taron na yau (Asaba) saboda haramtacce ne kuma yanzu kumai ya lafa.

Ba a samu wata arangama tsakanin bangarorin ba duk da cewa da farko ’yan sandan sun kama wasu masu zanga-zangar amma daga baya suka sake su.

Masu zanga-zangar sun fito ne sanye da bakaken kaya da ke alamta juyayin halin tashin hankalin da ake ciki a Kudacin.

Limis Alpha, daga cikin jagororin zanga-zangar ya ce zanga-zangar lumana ce domin bayyana damuwar jama’ar Kudancin Kaduna.

“An hana mu gudanar da zanga-zangar domin tun kafin mu taru motoci 15 zuwa 20 na ’yan sanda dauke da makamai sun isa wurin.

“Bukatarmu ita ce a samu kwanciyar hankali a kasa. Mun gode Allah komai ya tafi lafiya domin mu da ’yan sandan mun fahimci juna”, inji shi.

Ya ce sun tsara yin zanga-zangar ne ta hanyar daga kwalaye masu dauke da sakonni ba tare da yin jawabai ba, domin shuru ma magana ce.

Kudancin Kaduna ya dade yana fama da tashin-tashina musamman hare-haren kabilanci da daukar fansa da ya yi ajalin mutane da dama.