Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da kisan gillar da aka yi wa hakimin kauyen Maigari, a Karamar Hukumar Rimin Gado da ke jihar.
An ruwaito cewar wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kashe Alhaji Dahiru Abbas mai shekara 70 a gidansa a ranar Lahadi.
- Liverpool ta yi kaca-kaca da United a Anfield
- A tuhumi ’yan siyasa kan karancin abinci a Najeriya —Obasanjo
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
“A ranar Lahadi da misalin karfe 3:05 na safe ne aka samu rahoton cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki gidan Abbas, Hakimin Maigari, a Karamar Hukumar Rimin Gado a kokarinsu na yin garkuwa da shi.
“Wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun harbi basaraken a kirji sannan an garzaya da shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano inda a nan rai ya yi halinsa,” in ji shi.
Kiyawa ya kara da cewa an kara zage damtse domin kamo wadanda suka tafka aika-aikar.
Aminiya ta ruwaito cewa Maigari Abbas shi ne mahaifin Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado, Munir Dahiru Maigari.