✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun shiga karkashin mota don ceto ’yar kyanwa da ta makale

Rundunar ’Yan sandan New York a Amurka  ta nuna wani hoton jarumtar da jami’anta hudu suka nuna  wajen ceto ran wata ’yar kyanwa da ta…

Rundunar ’Yan sandan New York a Amurka  ta nuna wani hoton jarumtar da jami’anta hudu suka nuna  wajen ceto ran wata ’yar kyanwa da ta makale a kasar injin wata mota.

’Yan sandan na shiyya ta 32 a garin Harlem, su bakwai ne suka samu rahoton ’yar kyanwar ta makale nan da nan suka hada gwiwa da rundunar jami`an tsaro na musamman zuwa yankin da motar take.

’Yan sandan yankin sun sanar da hakan ne a shafinsu na Tiwita tare  da hotunan ’yan sandan lokacin da suke kokarin ceto ’yar kyanwar a karkashin motar don ceto rayuwarta kamar sauran dabbobi saboda zaman ’yar kyanwar a cikin injin motar na iya sanadiyyar rasa ranta.

“Zaman kyanwar a injin motar bai dace ba,” in ji ’yan sandan.