✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun rushe maboyar masu garkuwa da kama 4 a Akwa Ibom

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta kama wasu mutum hudu da ake zargin masu yin garkuwa da mutane ne da suka addabi Karamar Hukumar…

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta kama wasu mutum hudu da ake zargin masu yin garkuwa da mutane ne da suka addabi Karamar Hukumar Eket da kewayenta  sannan suka rushe inda suke aje mutanen da suka sace.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Odiko MacDon, a yau Juma’a ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Laraba da ta gabata a garin Ikot Ubo da ke karamar hukumar Nsit Ubium ta jihar Akwa Ibom, daya daga cikin masu garkuwan ya tsere da raunin harbin bindiga sakamakon musayar wuta da ka yi da ‘yan sandan.

SP Odiko, ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun kubutar da wata mata da aka yi garkuwa da ita mai suna Misis Glory Samuel, yanzu haka tana wani asibiti a garin Eket tana jinya.

Mijin Misis Glory, mai suna Mista Samuel Ekerenam ya ce ya biya Naira miliyan 3 a matsayin kudin fansa amma duk da haka suka ki sakinta sannan suka bukaci karin Naira miliyan 17 kafin su sako ta.