✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kwance wani abin fashewa a Kano

Hanyar dai ita ce ta mahadar matafiya da ke shiga Kano daga jihohin Jigawa da Bauchi da kuma Yobe.

A garin Jogana da ke Karamar Hukumar Gezawa a kusa da birnin Kano, an shiga halin firgici bayan da aka gano wani abin fashewa a kauyen Aujirawan Alkali.

Rahotanni sun ce sai da masu amfani da titin Kano zuwa Hadeja wanda ya bi ta garin sun rika canza hanya saboda kaucewa bacin rana da gudun kada abin fashewar ya tashi da su.

Hanyar dai ita ce ta mahadar matafiya da ke shiga Kano daga jihohin Jigawa da Bauchi da kuma Yobe.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa ’yan jarida a Kano ranar Juma’a.

Ya ce tuni dai jami’an rundunar suka sami nasarar kwance sinadarin, inda ya ce kuma sun dukufa da bincike domin gano wadanda ke da hannu a ciki.

Kiyawa ya ce wani mazaunin yankin ne ya gano sinadarin lokacin da ya shiga cikin daji domin yin fitsari da misalin karfe 5:00 na safiyar ranar Juma’a.

Ya ce ganin hakan ne ya sa mutumin bai yi wata-wata ba wurin sanar da ’yan sanda wadanda su kuma suka tashi jami’ansu zuwa wurin.

“Da jin haka ne Kwamishinan ‘Yan Sanda ya umarci sashen rundunar da ke da kwarewa wajen kwance abubuwan fashewa karkashin jagorancin CSP Haruna Ismail zuwa wurin sannan suka sami nasarar kwance shi da kayan aikinsu,” inji kakakin.