✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kwace motocin gwamnati a gidan tsohon gwamnan Zamfara

Majiyar Aminiya a gidan Matawalle da ke Gusau, ta ce a ranar Juma'a jami'an tsaro suka ce gidan suka kwato motocin

’Yan sanda sun kai samame gidan tsohon gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, inda suka kwace motocin alfama na gwamnati da ake zargin ya yi awon gaba da su bayan ya sauka daga mulki.

Majiyar Aminiya a gidan Matawalle da ke unguwar GRA a Gusau, hedikwatar jihar, ta ce a ranar Juma’a jami’an tsaro suka ce gidan suka kwato motocin.

Aminiya ba ta tantance iya adadin motocin da aka kwace daga gidan Matawalle ba, amma majiyarmu ta tabbatar mana cewa jami’an tsaro sun yi awon gaba da motocin alfarma guda hudu daga gidan.

Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sanda Jihar Zamfara, ASP Yazdi Abubakar, domin samun karin bayani kan wannan dambarwar amma ya kasa samun jami’in.

Shi ma jami’in yada labaran Matawalle, wato Zailani Bappa, mun kasa samun sa, har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.

Aminiya ta ruwaito yadda kwana biyu bayan rantsar da sabon gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya zargi Matawalle, da yin awon gaba da motocin alfarma guda 17 na ofishin gwamna da na mataimakin gwamna da cewa mallakinsa ne.

Gwamna Lawal ya ce,  hatta kayan ofis da talabijin da kuma murahun girkin gidan gwamnati, Matawalle bai bari ba.

A ranar Asabar ya ba wa tsohon gwamnan wa’adin kwana biyar ya dawo da duk kadarorin gwamnatin da ya yi awon gaba da su.