✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kubutar da mutum 8 daga hannun masu garkuwa a Katsina

An kubutar da su ne bayan musayar wuta da jami’an tsaro.

Jami’an ’yan sanda a Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina sun yi nasarar kubutar da mutane takwas daga cikin 11 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a hanyar Batsari zuwa Jibiya da ke Jihar.

An dai sace mutanen ne a daidai kauyen Kabobi da ke hanyar, inda maharan suka yi awon gaba da dukkan fasinjojin dake cikin farar mota mai kirar Golf.

To sai dai jami’an ’yan sandan yankin karkashin Baturen ’Yan Sandan Batsari sun kubutar da takwas daga cikinsu ranar Juma’a, 23 ga wannan watan Yulin 2021, jim kadan da samun labarin harin.

Mutum takwas din da aka kubutar daga hannun masu garkuwar.
Mutum takwas din da aka kubutar daga hannun masu garkuwar.

Mutane takwas daga cikin 11 da aka sace sun sami nasarar kubuta ne bayan an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da su.

Har ila yau, ’yan sandan sun kuma bi sawun sauran mutane ukun da ake zaton suna hannun ’yan bindigar.

Daga cikin mutanen da aka ceto har da wani dattijo mai kimanin shekara 70 da kuma wani jariri mai watanni takwas da haihuwa.

Dukkan mutanen da aka ceto dai ’yan asalin kauyen Garin Inu ne da kuma Unguwar Turaku da ke cikin Karamar Hukumar Batsari ta Jihar ta Katsina.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar hakan a wata sanarwar da ya raba wa manema labarai.