✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kubutar da mutum 15 daga gidan mari

’Yan sandan Jihar Adamawa sun tabbatar da tsirar da mutum goma sha biyar da aka tsare a gidan mari. ’Yan sandan sun tabbatar da cewa…

’Yan sandan Jihar Adamawa sun tabbatar da tsirar da mutum goma sha biyar da aka tsare a gidan mari.

’Yan sandan sun tabbatar da cewa mutum goma sha biyar din da aka samu a gidan sun kunshi manya goma sha uku da kananan yara biyu inda aka dauresu da sarka kuma ana cin zarafinsu, kuma an samu gidan ne Unguwar Wuro Hausa da ke cikin Karamar Yukumar Yola ta Kudu.

’Yan sanda sun ce da suka samu labarin gidan da kuma yadda ake azabtar da mutanen da ke gidan, sai suka yi musu ziyarar ba zata a daren Talata inda suka tsirar da wadannan mutum goma sha biyar da aka tsare a matsayin yi musu horo.

Kakakin ’yan sandar Jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya bayyana faruwar haka  a ranar Laraba ga manema labarai, ya ce wadansu daga cikin mutanen sun shafe tsawon shekara daya a cikin gidan inda ya kara da cewa manyan daga cikin mutanen da kanana na da kimanin shekara ashirin da biyu zuwa arba’in da shida.

Ya ce an daure su da sarka sannan ana wulakanta su da musu duka ba tare da ba su abinci ba ko kuma kulawa ga lafiyar jikinsu ba.

Ya ce an kama wadanda ke da hannu a cikin wannan aika-aikar inda ya ce akwai wani Bappa Mallan da wadansu uku wadanda suke da hannu a cikin wannan harkar sannan ya ce sun karya doka kuma za a hukunta su.