✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 3 a harin caji ofis

An kashe sufeton dan sanda a harin na tsakar dare.

’Yan sanda sun bindige mutum uku daga cikin wasu ’yan bindiga da suka kai hari a caji ofis a Jihar Imo.

Maharan sun cinna wa caji ofis din wuta tare da jefa abubuwan fashewa; Ganin haka ne ’yan sanda suka yi dauki ba dadi da su, suka aika uku daga cikinsu lahira.

Jami’in Hulda da Jama’a na ’yan sanda a Jihar Imo, CSP Mike Abattam ya ce, “Da misalin karfe 9:35 na dare, ranar Alhamis, ’yan bindiga suka kai farmaki suna jefa ababen fashewa a kan rufin caji ofis din Orsu, wanda hakan ya haddasa gobara.

“Wasu daga cikin ababan hawa da aka ajiye a harabar caji ofis din sun kama da wuta.

“Nan take jami’anmu suka bi su aka fara musayar wuta, aka kashe uku daga cikinsu, aka kwace bindigoginsu, sauran kuma suka tsere zuwa cikin daji da raunukan harbi.”

Sai dai ya ce “abin takaici shi ne wani Sufeton dan sanda ya rasa ransa a harin.