Rundunar ’Yan Sanda reshen Jihar Sakkwato ta samu nasarar kama ’yan bindiga 57 yaran kasurgumin dan bindigar nan, Bello Turji a wani farmaki da suka kai masu a Kananan Hukumomin Goronyo da Rabah da Illela na Jihar.
Jami’an rundunar na musamman karkashin jagorancin Mataimakin Babban Sufeton ’yan sanda, DIG Zaki M. Ahmad ne suka yi nasarar wannan farmakin inda suka kama mutum 37 da ake zargin ’yan bindiga ne sai wasu 20 da ake zargi da hulda da ’yan bindigar kai tsaye.
A taron manema labarai da aka gudanar a Sakkwato, Zaki Ahmad ya ce sun samu nasarar kama mutanen ne a garuruwan Gudugudu, Illela, Heli, Goronyo, Mayel, Sakanau, Kuka, Zangon Isu, Tsamaye, Dunawa, Tangaza, Isa, Bungo, Sangari da sauransu.
DIG Zaki ya kuma ce sun kama ’yan bindigar ne a wurare daban-daban kan alakarsu da samamen da ake yi, sannan sun kama miyagun makamai a hannunsu.
Ya ce, “Dukkan wadanda aka kama suna da alaka da ayarin sanannen dan bindigar nan Bello Turji, kuma sun fadi suna aikata miyagun laifuka na fashin daji.
“Haka kuma ana cigaba da bincike kan lamarin, da zaran an kammala za a kai wadanda ake zargi gaban shari’a,” a cewar Zaki.
Ya ce daga cikin abubuwan da aka samu a hannunsu akwai shanu 150 da bindigun AK-47 guda 32 da harsasai 2,700 da babbar bindiga mai harbo jirgi daya da babur biyu da motoci uku da wayar salula 16 da Katon 10 na allurar Penta da sauransu.
A cikin manyan ’yan bindigar, a cewarsa, akwai likitansu, Abubakar Hashimu Kamarawa da mai kai masu makamai Musa Kamarawa da sauransu.