Hukumar ‘yan sandan Najeriya tare da hadin gwiwar rundunar sojojin saman Najeriya sun kama mutum biyu da ake zarginsu da kashe tsohon babban hafsan tsaron Najeriya Alex Badeh (mai ritaya).
Majiyarmu ta samu rahoton a jiya Laraba cewa, a yau Alhamis ne za a bayyana wa manema labarai wadanda ake zargin su da kisan a hedkwatar tsaron Najeriya da ke Abuja.
Rahoton na bayyana cewa, an samu shadun da ke nuna cewa, wadanda ake zargin nada hannu wajen kisan Badeh za a bayyana cikakken rahoton idan aka gabatar da mutanen da ake zargin.