✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama wanda ya yiwa ‘yarsa ciki a Ogun

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekaru 42 mai suna Taufik Oyeyemi da ake zargi da yiwa ‘yarsa ciki budurwa mai…

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekaru 42 mai suna Taufik Oyeyemi da ake zargi da yiwa ‘yarsa ciki budurwa mai shekara 16.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa jami’ansu sun kama mutumin ne bayan da mahaifiyar yarinyar wacce ta rabu da mijin nata, ita ta shigar da kara bayan da ‘yarta ta shaida mata cewa mahaifin ta ya yi mata ciki ya kuma kaita an zubar da cikin lamarin da ya sanya take ta zubar da jini.

Ya ce, rundunar ‘yan sandan na binciken lamarin za kuma a gurfanar da wanda ake zargin a kotun.